Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Kungiyoyin Ma’aikata Zasu Tsunduma Cikin Yajin Aiki

nlc2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar kwadago ta Najeriya da hadin gwiwar wasu kungiyoyi zasu tsunduma cikin yajin aiki sakamakon rashin biyan kayyadajjen albashi na Naira 30,000 har zuwa yanzu.

Hakan ya biyo bayan duk da daga kafar da suka yi akan wa’adin da sukabayar daga 4 ga watan Satumba zuwa 16 ga watan Satumba don a samu a sanar da shugaba Muhammadu amma har yau ba’a tsaida matsaya guda daya ba.

Yayin taron wanda shugaban ma’aikata na kasa Winifred Oyo-Ita ya jagoranta ya bayyana cewa gwamnati ta daga daga kashi 9.5 zuwa kasha 11 daga mataki na 7 zuwa na 14 sai kashi 6.5 daga mataki na 15 zuwa 17.

Inda ma’aikata suka dage kan cewa gwamati ta kara albashin ma’aikata daga mataki na 7 zuwa na 14 da kashi 30, sai masu mataki na 15 zuwa 17 da kashi 25.

Kungiyoyin sun bayyanawa manema labarai bayan taron cewa basuji dadin abun ba kuma gwamnati kawai tana wasa da hankalinsu ne.

Haka nan sun kara da cewa kwanan nan zasu sanar da yan Najeriya inda suka tsaya tunda gwamnatin tarayya bata dauki abun da mahimmmanci ba inda suke zargin akwai wata kullalliya.

Related stories

Leave a Reply