
Kwamitin zaben na kungiyar ‘yan jaridu reshen jihar Borno ya daga zabe da sati daya.
Rahoton ya fito daga sakataren kungiyar Muhammad Kabir Tahir inda yace baza a gudanar da taron ranar shirin da biyar ga wan nan watan ba kamar yadda aka tsara a farko.
Kwamitin yace bai so hakan ya faru ba kuma yana bawa ‘yan kungiyar hakuri inda ya bukaci ‘yan takarar dasu ci gaba da gudanar da yakin neman zaben su.

