Najeriya: Kungiyar Yan Jaridu Ta Kasa Reshen Jihar Borno Ta Nuna Damuwarta Kan Hare-Hare A Jihar

NUJ
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar Borno wato NUJ ta nuna matukar damuwarta game da hare-hare da yan ta’adda ke kaiwa kan fararen hula da basuji ba basu gani ba, musamman na yan kwanakin nan a kananan hukumomin Nganzai, Kaga, Bama da Kukawa.

Kungiyar tayi kira ga al’ummar gari da su taimakawa jami’an tsaro da bayanai a duk lokacin da suka ga za a samu barazana akan harkan tsaro.

Haka zalika kungiyar ta yabawa sojoji saboda sun rage karfin yan Boko Haram, amma sunyi kira ga sojojin dasu dada azama wurin kare matsugunan yan gudun hijira da sauran kauyuka da aka kubutar daga hannun yan ta’adda.
A karshe, kungiyar tayi kira ga yan Boko H
aram da su rungumi zaman lafiya, su tattauna da gwamnatin tarayya kan bukatunsu.

Related stories

Leave a Reply