Najeriya: Kungiyar ‘Yan Jaridu Reshen Jihar Borno Tace Zasu Dinga Duba Ayyukan Gwamnatin Jihar

NUJ
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban yan jaridu na jihar Borno, Bulama Talba ya bayyana cewa yan jaridun jihar zasu dinga kula da ayyukan da gwamnati takeyi don kawo karshen talauci a jihar.

Talba ya bayyana hakan a taron da sukayi na 14 a Pinnacle Hotel dake birnin Maiduguri.

Ya kara da cewa tattalin arzikin da ake fama dashi a kasar ya saka mutane da dama a cikin kangin talauci kuma na jihar ta Borno ya fi kamari ne saboda rikicin ta’addanaci da aka sha fama dashi a yankin inda ake cikin shekara ta 11.

Ya kara da cewa aiki yan jarida ba wai kawai su bada labari, su nishadantarko su ilmantar bane ya kamata su dinga duba ayyukan gwamnati.

Wadanda sukayi jawabi yayin taron sun hada da Darakta janaral na NOA Dr Garba Abari, wadanda suka wakilci Madam Maryam Uwais mai bawa shugaba Buhari shawara kan ayyukan more rayuwa, shugaban CAN da Malamai.

Related stories

Leave a Reply