Najeriya: Kungiyar Masu Fafutuka Na Zamfara Sun Kaiwa Buhari Ziyara

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa mahukuntan tsaro zasu kare rayuwar mutane da dukiyoyinsu.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da wadan nan suka wakilci kungiyar masu fafutika na Zamfara a fadar gwamnatin kasar dake Abuja ranar Litinin.

Ya kara da cewa jami’an sojoji da yansanda sun dauki tsauraran matakai don dubaa ayyukan wadanda suke kokarin tada hankalin al’umma a yankunan ciki harda hana manoma zuwa gona.

Haka nan ya bayyana cewa yana samun rahoton duk abinda yake faruwa a kullum daga jami’an dake fagen da kuma sarakunanan gargajiya.

San nan ya bayyana abin da yake faruwa a matsayin abun takaici kuma ya kirayi shugabannin al’umma da sarakuna dasu dinga lura da al’amuran mutane don su taimakawa jami’an tsaro da bayanai.

Shugaban ya yabawa sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, kan yadda yake kula da sha’anin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *