Najeriya: Kungiyar Kwadago Reshen Jihar Borno Sun Bukaci Da A Biya Hakkokin Ma’aikata

nlc2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar kwadago reshen ta ta jihar Borno dake Arewa maso gabashin najeriya ya kirayi gwamna mai barin gado Kashim Shettima da ya biya hakkokin ma’aikatan da sukayi ritaya tun shekarar 2013 wanda kudin ya kai kimanin Naira biliyan 20.

Ma’aikatan sun kirayi gwamnatin da ta yi kokari ta biyasu duk hakkokinsu na da dana yanzu a kananan hukumomi 23 inda wasu suna bin kashi 20 wasu kuma kashi 60.

Yayin da yake Magana a gurin bikin zagayowar ranar ma’aikatan na shekarar 2019 a Maiduguri, sabon shugaban kungiyar Bulama Abiso yace abinda yafi ci musu tuwo a kwarya shine rashin biyan hakkokin ma’aikatan da sukayi ritaya tun shekarar 2013.

Ya kara da cewa suna kiran gwamnan mai barin gado da ya biya kudaden kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Abiso kuma bayyana cewa suna kiran gwamnati da ta biya kudaden hutu dana Karin girma ga ma’aikatan jihar wanda aka dena shekara 3 da suka wuce.

Haka nan akwai kananan hukumomin da har yanzu suna bin kayyyadajjen albashi na Naira 18,000, akwai kuma wadanda har yau basu taba amfana da kayayyadajjen albashin na Naira 18,000 har yau ba, inda yace har yanzu akwai malaman makaranta da suke karbar Naira 10,000 da 11,000.

Wakilin gwamnan, shugaban hukumar ma’aikata ta jihar Muhammed Hassan, ya bayyana cewa gwamanti na sane da bukatun ma’aikatan.

Related stories

Leave a Reply