
Kungiyar gamayyar faraen hula sunfita zanga-zanga a jihar Osun sakamakon Karin kudin wuta dana man fetur.
Zanga zangar ta fara daga gurin shakatawa na Freedom Park Osogbo da karfe 8 na safe inda dubbban mutane suka fito suka tare hanyoyi.
Sun fita bakin tituna dauke da alluna da akayi rubutu da dama kamar haka mungaji a dawo da kudin da, na wuta dana fetur.
Haka nan sun koka da sabon Karin wutar da na man inda sukace gwamnatin tarayyar bata yi tunani ba.
Dandal Kura ta gano cewa anyi ta Karin man akai akai cikin wata uku daga watan juni, yuli , Augusta da Satumba.
