Najeriya: Kotun Koli Ta Bayyana Buhari a Matsayin Wanda Ya Samu Nasara

president-muhammadu-buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kotun koli tayi na’am da hukuncin da mai shari’a Justice Mohammed Garba ya yanke ranar 11 ga watan satumba a kotin kara ta zabubbuka wadda ta bayyana shugaba MuhammaduBuhari a matsayin wanda ya samu nasara a zaben day a gabata. 

Kotun mai mutane 7 wadda shugaban shari’a na kasa Tanko Mohammed yake jagoranta yace sun amince da rashin ingancin karar da Alhaji AtikuAbubakar da jam’iyyar sa ta ,PDP ta gabatar.

Mohammed din yace sun yita duka sharia’r fiye da sati 2, kuma basu gano matsalolin dad an takarar ta PDP ya kai kara akai ba kan zaben da aka gudanar ranara 23 ga watan Feburairu.

Atiku da PDP sun kalubalanci jami’an tsaro da jam’iyyar APC wajen gudanar da ayyukan rikici, siyan kuri’u, dagwale da sauransu a jihohi kamar Borno, Yobe, Niger, Katsina, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Kano, Gombe da Kebbi. 

Related stories

Leave a Reply