
Kotun dake saurarn karan zaben yan majalisun tarayya ta soke zaben da akayi wa sanata Dino Melaye mai wakiltan jahar kogi ta yamma a majalisar dattijai.
wanda ya shigar da karan Senator Smart Adeyemi yayi korafin cewa zaben da kayi wa Dino melaye cike yake da kura-kurai da kuma karan tsaye ga dokokin zaben kasar nan.
mai shari’ah A. O. Chijioke tare da masu taimaka masa guda 2 sun amince da cewa a sake sabon zabe a mazabar dattijai ta jihar kogi ta yamma.

