Najeriya: Kotu Ta Kulle Mataimakin Daraktan Hukumar INEC Shekara 6 A Jihar Jigawa

court
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mai shari’a Yusuf Birnin-Kudu na babbar ktun dake jihar of Jigawa wadda take zamanta a Gumel ta yankewa mataimakin Daraktan hukumar INEC Auwal Jibrin, hukuncin shekara shida a gidan yari sakamakon mallakar abubuwa ba bias ka’ida ba.

An yanke musu hukunci shi da wani mai suna Garba Ismaila wanda aka daure shekara bakwai saboda karbar dala miliyan 115.010 daga cikin kudaden da tsohuwar Ministar mai ta kasa Diezani Alison-Madueke ta kwasa yayin zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

An yanke wa mutanen 2 hukunci ranar juma’a bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta mika su daga ofishinsu dake Kano.

Mai Magana da hukumar EFCC na rikon kwarya Tony Orilade ne ya bayyana hakan yayin da ya fitar da rahoton daga Abuja on Sunday cewa mutane biyun sun karbi Naira miliyan 45 cikin Naira miliyan 250 wanda aka tura jihar Jigawa State to kan zaben 2015.

Related stories

Leave a Reply