
Kotun daukaka kara ta birnin tarayyar Najeriya Abuja ta kori karar da ake tuhumar shugaba Muhammadu Buhari kan takardun karatun shi.
A zaman mutuum uku wanda mai shari’a Atinuke Akomolafe-Wilson yake jagoranta ya yanke cewa shari’ar ba akan lokaci take ba tunda ba lokaci bane na kafin zabe.
Masu karar Kalu Kalu, Labaran Ismail da Hassy Kyari el-Kuris sun zo kotun
daukaka karar bayan babbar kotun birni ta kori karar su kan cewa bata cikin lokacin da ya dace.
Mohammed Idris, wanda ya karanta hukuncin a madadin kotun ya bayyana cewa kotun tayi amfani da sashi na 285 (9) na 1999 inda yace an kawo shari’ar ba kan lokaci ba inda aka ce akai karar cikin kwanaki 14 days kafin lokacin zaben.
