Najeriya: Kotu Ta Bada Belin Babagana Abba Dalori

dalori
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babbar kotu dake babban birnin tarayyar Najeriya Abuja wadda take Kwali karkashin mai shari’a Simon Venchek Gaba ta bada belin injiniya Babagana Abba Dalori na kamfanin Galaxy Transport and Construction Limited.

An zargi Dalori da damfara inda ya kirkiri hanyar samar da kudin bogi don kiran wasu a arewa maso gabashin Najeriya.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ce ta kama shi inda a farko aka kama shi aka kaishi gidan yari Kuje.

Mai shari’a Gaba bayan muhawara da lauyar EFCC Maryam Ahmed da Joe Kyari Gadzama SAN inda ya kirayi da bada belin shi hade da biyan Naira Miliyan 5.

Mai shari’ar ya bukace shi da ya kawo mutane biyu wadanda zasu tsaya da gidaje kamar yadda kotun ta bukata.

A rahoton da Barrista N. A. Dammo ya hada ya roki kotu da tasa EFCC ta sake shi ko ta samishi tarar da zai biya.

Related stories

Leave a Reply