Najeriya: Kotu Na Cigaba Da Tsare Shugabar Wata Makarantar Sakandire A Jihar Borno

borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

BY:BABAGANA BUKAR WAKIL NGALA

Ana cigaba da tsare shuabar makarantar Dala Standard secondary school mai suna Josephine Udeh a gidan yari sakamakon damfarar fiye da Naira miliyan 5 daga hannun wadanda suke so su zana jarabawar WAEC a makarantar ta.

Madam Udeh wadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta kai gaban mai shari’a Aisha Kumalia ta babbar kotu birnin Maiduguri, an bayyana cewa ta damfari dalibai 284 fiye da Naira miliyan 5.

Josephine Udeh ta damfari mutanen 284 a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018 winda ta tashi da kudi Naira 5, 059,000. Inda tace zata biya musu kudin jarrabawar WAEC don ta damfaresu wanda ya saba a kundin tsarin Mulki a sashi na 1(2) da hukunci a sashin 1(3) na kundin tsarin mulkin 2006.

Ran dalibar y abaci bayan da sukaje guraren da zasu zana jarrabawar akace ba sunan su, shine suka aikawa hukumar EFCC korafi.
Lauya mai kare mai laifin Barrister Aminu Sani ya roki da a bada belinta a zaman da za’a sake ranar 14 ga watan Mayu na shekarar 2019.

Related stories

Leave a Reply