Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Kimanin Yan Gudun Hijira 7000 Ne Suke Kwana A Waje A Garin Bama Dake Jihar Borno – Edward Kallon

kallon
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban tsare-tsaren bada agaji na majalisar dinkin duniya a Najeriya Mr Edward Kallon ya bayyana cewa cikin yan gudun hijira 38,000 dake sansanin yan gudun hijra a Bama dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya 7000 na kwana a filin Allah ba tare da dakuna ba.

Kallon ya bayyana hakan yayin gabatar da labarai ga manema labarai tare da mataimakin gwamnan jihar Usman Kadafur da kuma jagorar hukumomi masu zaman kansu wanda Mrs Ibukun Awosika ta jagoranta bayan sun zagaya zuwa wasu sansanonin yan gudun hijra a birnin Maiduguri.

Ya kara da cewa baza a yadda da halin da yan gudun hijirar suke ciki ba idan aka duba yadda ba’a bada karfi wajen rayuwarsu.

Ya kuma bayyana cewa majalisar dinkin duniya da hukumomi masu zaman kansu basa mai-maita ayyukan da sukeyi sai dai suna hada karfi da gwamnatin jihar da kuma hukumar Northeast Development Commission (NEDC).

Kallon ya bayyana cewa an hada dala miliyan 80 da za’a yi amfani da su wajen samar da ruwa, gyaran muhalli, lafiya, kariya, gidaje, ilimi da sauransu.

Shugabar hukumomi masu zaman kansu wadda take shugaba ce a bankin First Bank Of Nigeria Mrs Ibukun Awosika , ta bayyana cewa nasarar hukumomi masu zaman kansu itace su saka duk yan Najeriya a ayyukan da suke daukar nauyi.

Awosika ta kara da cewa wan nan na daya daga cikin kungiya ta farko da ta hada kai da majalisar dinkin duniya wajen bada taimako ga mutane da kuma sake gina arewa maso gabashin Najeriya.

Yayin da yake jawabi mataimakin gwamanan jihar Usman Kadafur ya yabawa majalisar dinkin duniya wajen hadin kai da hukumomi masu zaman kansu don bada taimako a yankunan jihar Borno da ake fama da rikici.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar zata ci gaba da samar da tsaro ga mutanen yankin saboda idan ba zaman lafiya baza a samu cigaba ba.

Related stories

Leave a Reply