Najeriya: Kimanin Mutane 244 Suka Kamu Da Cutar Cholera A Jihar Adamawa

IDP-Camp-Cholera_2-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An samu kimanin 244 na masu dauke da cutar Cholera cikin wata daya a jihar Adamawa inda ya nuna cewa an samu Karin 168 daga 76 da ake dasu a Yola ta Arewa da Yola ta kudu da yankin Girei dake jihar ranar 17 ga watan Yuli na shekarar 2019.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a Yola Daraktan lafiya matakin farko Dr. Bwalki Dilli ya bayyana cewa wadanda suka rasu sun kai mutuum 3 a yanzu.

Ya kara da cewa an samu kari a cikin wata daya wanda da ake tsammanin raguwar su tunda jami’an lafiya na aikin bada magani ga wadanda abin ya shafa.

Ya kara da cewa suna samun taimako daga gurare kamar WHO da UNICEF.

Related stories

Leave a Reply