Najeriya: Kamfanonin MTN Da DSTV Sun Rufe Ofisoshinsu A Jihar Kano

mtn
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sakamakon martini da kasar Najeriya ta mayar na toshe duk wata hada-hada tsakanin kasuwancin kasar data afirka ta kudu, an sake rufe ofishin kamfanonin MTN dana DSTV dake jihar Kano.

Wata majiya ta tabbatar da cewa an rufe ofisoshin DSTV na Nasarawa dake GRA sakamakon mamaya da yan tsaro sukayi wa wajen haka kuma a halin yanzu zirga-zirga ya dan ja baya a titin Zoo road inda babban shagon nan na Shoprite yake.

Rikici tsakanin Najeriya da afirka ta kudun dai yayi tsamari, sannan ana hasashen rikicin zaifi shafan arewa maso gabashin kasar.

Related stories

Leave a Reply