Najeriya: Jirgin Ruwa Ya Kife A Jihar Neja

Niger State
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kimanin mutane 15 ne suka rasa rayukansu inda wasu da dama suka samu raunuka, wasu suka bata bayan da wani jirin ruwa ya kife a karamar hukumar Borgu dake jihar Neja.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa wadanda abun ya ritsa dasu sun dawo ne daga kasuwar Warrah dake da iyaka da kauyen dake karamar hukumar Ngaski dake jihar Kebbi.

Rahoton ya kara da cewa an samu hatsarin ne saboda rashin kyan yanayi wanda yayi sanadiyyar da yasa jirgin ya daki wata bishiya dake cikin kogin Malale yayin da sukayi tsakiyar tafiyarsu.

An samu gawar mutuum 15, an ceto mutum 2, san nan da yawa ba’a gansu ba. Darakta Janaral na hukumar bada agajin gaggawa na jihar, Alhaji Ibrahim Inga ya tabbatar da faruwar lamarin.

Haka nan ya kara da cewa jirgin na dauke da mutane 50, inda har yanzu direbobin nan nan na neman ragowar da ba’a gani ba.

Related stories

Leave a Reply