Najeriya: Jami’an Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Boko haram Da Dama

armytroopssmall
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Runduna ta 3 karkashin Operation LAFIYA DOLE dake Super Camp a Monguno sun kashe yan ta’addan Boko haram da dama yayin zagaye a kan titin Monguno-Mairari zuwa Gajiram a Arewacin Borno.

Mai Magana da yawun rundunar Col. Sagir Musa ne ya bayyana hakan ranar juma’a. Ya bayyana cewa masu sintirin sun hadu da yan ta’addan inda suka sukayi musayar wuta suka kashe wasu da dama wasu kuma suka tsere da raunuka.

Haka nan jami’an sun samu makamai da dama inda 3 daga ciki suka rasa rayukansu. Tuni dai aka garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti don karbar magunguna.

Jami’an na cigaba da kakkabe yankin gaba daya kuma kakkabe ragowar yan ta’addan daga yankin.

Related stories

Leave a Reply