
Jami’an Civil Defence Corps wato NSCDC dake jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya sun cafke wani mai suna Aliyu Muhammed dan shekaru 24 da zargin mai samar da abubuwan fashewa ga yan kungiyar Boko Haram a Maiduguri.
Kwamnadan rundunar Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na NAN a Maiduguri yayin wata hira da sukayi dashi.
Abdullahi yace jami’ansa sun kama wanda ake zargin ranar 25 ga watan Afirilu bayan wasu bayanan sirri da suka samu akan hanyarsa ta kai kayan hada abun fashewar gay an kungiyar ta Boko Haram.
Ya kara da cewa wanda ake zargin na kai musu batirin wayar tafi da gidanka, agogo, da kwamfuyuta wajen shirya abun yadda zai kashe mutane da dama.
Wanda ake zargin yana aiki da babur mai kafa uku a cikin gari, kuma ya taimakawa yan ta’addan wajen kai hare – hare da dama, san nan yana da asusun bankuna daban daban da yake karbar kudi har daga kasar Chadi.
Hukumar ta kama fiye da yan kungiyar Boko Haram 25 a shekara biyu ciki har da mata yan kunar bakin wake, haka nan sun sa kimanin 40 sun mika wuya ga jami’an tsaro.
Ya kuma bayyana cewa zasu mika Mohammed ga jami’an sojojin dake Maiduguri don bincike na musamman.
