Najeriya: Ilimin Almajirai Na Wuyan Gwamnatocin Jihohi – Buhari

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari y ace ba daidai bane a zargi gwamnatin tarayya game da daukar nauyin karatun Almajiranci, domin kuwa wannan alhaki ne da ya rataya wutan gwamnonin jihohi.

Buharin ya bayyana hakane ya yin da yake marabtan mambobin masu rajin cigaban ilimi a fadarsa dake birnin tarayya Abuja. Ilimin almajiranci dai wani tsari ne na koyon ilimin addini wanda ya shafi tattalin arziki da kuma makomar addinai a wasu jihohin arewacin kasar nan.

Hakazalika a ranar 12 ga watan Yuli shugaba Buhari ya yi watsi da wani rahoto na cewa gwamnatin tarayya takammala tsarin yin fatali da ilimin Almajiranci. Inda ya shaidawa tawagar cewa a tsarin doka gwamantocin jihohi ne keda alhakin inganta tasarin ilimin Almajiranci.

Har ila yau ya ce gwamanti ta ware naira biliyan 25 domin biyan malaman jami’a kudaden alawus-alawus din da suke bin gwamnati.
Tun da farko da yake jawabi mai magana da yawun ‘kungiyar Dr Bolariwa Bolaji, ya bayyana cewa a shirye ‘kungiyar take da ta yi hadin gwiwa domin dabbaka ‘kasar nan zuwa mataki na gaba.

Related stories

Leave a Reply