Najeriya: Hukumar Zabe Ta Jihar Adamawa Ta Daga Ranar Zaben Kananan Hukumomi Zuwa 7 Ga Watan Disamba

ADAMAWA
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar zabe ta jihar Adamawa ta daga ranar zaben kananan hukumomi daga ranar 9 ga watan Nuwamba zuwa ranar 7 ga watan Disamba inji shugabanta na jihar Alhaji Isa Shettima.

Shettima ya bayyana hakan a rahoton daya fitar ga manema labarai a Yola, inda yace dagawar ya zama dole saboda wasu kalubale.

Yayin da yake jawabi Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC Alhaji Ahmed Lawan yace jam’iyyar sa bata ji dadin wan nan batun ba amma ta karbe shi da kyakkyawar manufa.

Haka nan sakataren tsare-tsare na jam’iyyar PDP, Alhaji Hamza Bello yace jam’iyyarsa zata cigaba da gudanar da yakin neman zabe tunda an samu canji.

Related stories

Leave a Reply