Najeriya: Hukumar NAFDAC Zata Duba Kaya Da Magunguna Marasa Inganci

NAFDAC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta bayyana cewa za ta sa ido kan magunguna marasa inganci akalla ya koma kashi biyar cikin dari kafin shekarar 2025.

Darakta janar na hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana haka ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Ta kuma bayyana cewa bayanan ‘karshe da hukumar ta tatttara na magunguna marasa inganci shi ne  kaso 16.7 cikin dari.

A cewarta kaso 16.7 dahu kumar ta tattara shekaru sha hudu da suka gabata ne don haka akwai bukatar hukumar ta sake sa ido domin ‘kara gano magunguna marasa inganci a ‘kasar nan.

A ‘karshe Adeyeye ta bayyana cewa wajibi ne hukumar ta sa ido domin bada kariya ga lafiyar al’umma.

Leave a Reply