Najeriya: Hukumar Kare Hadura Ta Kasa Ta Rarraba Kayayyakin Agaji Ga ‘Yan Gudun Hijira A Jihar Kaduna

FRSC small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar kare hadura ta kasa ta rarraba kayayyakin agaji ga ‘yan gudun hijirar dake sansanin Mararaban Kajuru a jihar Kaduna.

Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Grace Peter ta bayyana cewa sun bada agajin ne don a rage wa mutane radadin dake damunsu na hare-haren da ‘yan bidigar suka kai musu a yankin.

hare-haren yayi sanadiyyar da mutane 10,000 suka rasa mahallansu a rahoton da aka fitar tsakanin watan Fabarairu da watan Mayu na shekarar 2019.

kayayakin sun hada da kayan abinci,abin sha, kayan sawa, kayan amfanin gida, sabulun wanka da wanki. inda suka ce sun raba kayan a sansanonin dake kasar gaba daya.

Peter, ta kirayi wadanda abin ya shafa dasu yi hakuri su yafe, kuma su dage da addu’oin Allah ya kawo musu sauki a yankin.

Yayin da yake jawabi shugaban Adara Development Association dake karamar hukumar Kajuru Mr Umar Tanko ya godewa hukumar kan taimakon.

Related stories

Leave a Reply