
Hukumar dake jigilar mabiya addinin kirista zuwa kasar Isra’ila ta bayyana cewa an rage kudin ta na shekarar 2019 daga Naira 731,000 zuwa Naira 715,000.
Sakatariyar hukumar mai rikon kwarya Esther Kwaghe ce ta bayyana hakan a Abuja yayin saka hannu kan yarjejeniyar kwangilar jigilar mutane da kamfanonin da kuma masu kula da mutanen na shekarar 2019.
San nan ta kirayi ma’aikatan da karsu bata alkawarin da aka dauka dasu don kula da matafiyan.
Yayin da yake jawabi shugaban hukumar Yomi Kasali ya bayyana cewa an rage kudin ne sakamakon sa bakin da jihohi da masu ruwa da tsaki suka yi.
Haka nan hukumar ta kula da matsanancin tattalin arziki da ake fama dashi a kasar da kuma yadda mutane da dama suke so su gudanar da ayyukan ibadar.
San nan ya kirayi masu jigilar dasu kula da yan Najeriyar cikin mutunci da girmamawa yayin gudanar da ayyukansu a kasar.
Baban Daraktan kamfanin Atlas Jet Nigeria Ltd, Ercument Filiz ya tabbatarwa hukumar cewa zasu gudanar da aikin yadda ya kamata a wan nan shekarar.
Kamfanonin da suka samu halartar taron sun hada da Tabar Tours, Tailor Made Tours, Atlas Jet Nigeria, Ophir Tours da kuma Hadur Travel.
