Najeriya: Hukumar Fasa Kauri Zata Fara Daukar Ma’aikata

By: Babagana Bukar Wakil

Hukumar fasa kauri ta kasar Najeriya tace zata fara daukar ma’aikata ranar laraba, inda zasu dauki mutum 3,200 don cike wasu gurabu a hukumar.

Hakan na cikin wani gyara da akayi a hukumar shekarau 4 da suka wuce karkashin shugabancin, Col. Hameed Ali rtd.

Yayin da yake yiwa manema labarai jawabi a babban ofishinsu, maitaimakin shugaban na bangaren kula da ma’aikata Umar Sanusi ya bayyana cewa lokaci yazo da bangaren kula da ma’aikatan yake aiwatar da abubuwan da suka kamata.

Ya kara da cewa daukar ma’aikatan ya samu karbuwa daga majalisar ministocin Najeriya, inda suka ce ya kamata a duba cancanta bawai yare, addini ko jihar da mutum ya fito ba don ayiwa kowa adalci.

Haka nan ya tabbatarwa jama’a cewa za’a bi tsarin daukar ma’aikatan da gaskiya kuma a bude kamar yadda hukumar daukar ma’aikata ta bayar.

Sanusi ya kara da cewa hukumar zata samar da duk abinda ya dace yayin gudanar da aikin kuma komai kyuta ne ga kowa ba tare da wani ya biya wani abu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *