Najeriya: Hukumar Bada Agajin Gaggawa Zata Karfafa Ayyukanta A Kasa Baki Daya

nema 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato nema ta bayyana cewa zata karfafa ayyukanta a kasa baki daya ta hanyar karfafa ingancin ma’aikata da daukar matakan gaggawa.

Yayin taron da hukumar ta kafa na ma’aikatanta na shekarar 2019 a Keffi dake jihar Nasarawa, Daraktan shiyyar Arewa ta tsakiya Bitrus Samuel, ya tabbatar wa mazauna birnin tarayya da ragowar jihohin da ke shiyyar cewa hukumar a shirye take ta dauki matakan gaggawa da ya dace.

Ya kara da cewa mahimmin burin hukumar shine ta karfafa ingancin ma’aikatan ta ta hanyar bada horo don ganin yadda ma’aikatan ke daukar matakan gaggawa zuwa mataki na gaba.

Haka nan wani kwararre Adekunle Oni ya kirayi gwamnatin tarayya data karfafa rayuwar ma’aikata da wadanda sukayi ritaya don kawo karshen yaki da cin hanci da rashawa.

Related stories

Leave a Reply