Najeriya: Gwamnonin APC Sun Gana Da Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC a fadar shugaban kasar dake Abuja.
Gidan radiyon Dandal Kura international sun gano cewa har yau ba a san makasudin taron ba har yanzu da ake hada wan nan rahoton.

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ne ya jagorancin gwamnonin. Dandal Kura ta gano cewa gwamnonin sun gana da shugaban kasar karo na farko bayan da ya samu nasara a sharia’ar da aka gudanar don taya shi murna.

Ragowar sune shugaban jam’iyya kwamared Adams Oshiohmole, sakataren gwamnatin kasar, Boss Mustapha da kuma shugaban ma’aikata Malam Abba Kyari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *