Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bawa Kamfanonin Sadarwa Umarnin Rufe Layukan Waya Miliyan 9.2

SIM CARDS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya ta bawa kamfanonin sadarwa umarnin rufe layukan waya miliyan 9.2 wadanda basu da ciikakken rahoto.

Hakan ya fito bayan da hukumar kula da da kafafen sadarwar wato NCC wanda ministan sadarwa Dr Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayar.

Idan za’a iya tunawa Pantami ya bawa hukumomi da ma’aikatun dasu mika sakamakonsu. Bayan ya bada dokar NCC ta bada nata sakamakon wanda ke dauke dayawan layukan wayan da basu da cikakken rigista kuma ana amfani dasu a kasar.

Haka nan hukumar ta bayyana a rahoton ta cewa layikan miliyan 9.2 basu da cikakkiyar rigista.
Dr Pantami ya bukaci NCC dasu tabbata sun rufe layukan duk da basu da rigistar.

Haka nan hukumar sadarwar sun bayyana cewa hakan zai kara rashin tsaro, kuma baza su yadda da duk wani rashin daukar mataki da hukumar sadarwar keyi ba.

Related stories

Leave a Reply