Najeriya: Gwamnatin Jihar Yobe Ta Amince Da Fitar Da N127, 187,270.00 Don Aikin Hajjin 2019

Gwamnatin jihar Yobe ta amince da fitar da kudi Naira 127, 187,270.00 don gudanar da ayyukan aikin da kula da alhazan jihar a Hajjin shekarar 2019.

Kwamishinan gidaje, yada labarai da al’adu Mala Musti ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Damaturu ranar laraba bayan da suka gudanar da taron.

Ya kara da cewa don su biya akan lokaci kafin ranar 30 ga watan Mayu 2019 yayin da za’a gama biyan kudin gwamnatin ta amince da biyan kudin.

Mahukuntan jihar sun amince da cigaban da aka samu da dokokin da aka kafa na karasar da aikin filin saukar jirgin saman na jihar yobe dake damaturu inda aka yanke kudi Naira 6,067,305,786.91

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *