Najeriya: Gwamnatin Jihar Borno Zata Hada Kai Da CEED Don Horar Da Matasa

Gwamnan jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya farfesa Babagana Umara Zulum yace gwamnatinsa zata hada kai da Centre for Entrepreneurial and Enterprise Development wato CEED dake jami’ar Maiduguri don a rage radadin talauci a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ranar 4 ga watan Yuni na shekarar 2019 yayin da mahukuntan jami’ar suka kai masa ziyara wadda shugaban jami’ar farfesa Aliyu Shugaba ya jagoranta don gaisuwar Sallah a fadar gwamnatin.

Gwamnan ya bayyana cewa zai dauki nauyin horaswar da kuma wasu ayyukan a jamiar don rage rashin aikin yi ga matasa don su dogara da kansu.

Farfesa Zulum ya kara da cewa gwamnatinsa zata kirkiro ma’aikatar kimiyya da fasaha don samun masalaha kam wasu matsaloli.

San nan zasu nemo meye asalin abinda ya haddasa Boko Haram, talauci, rashin ilimi, rashin hanyoyin samun tattalin arziki, shaye-shaye, canjin yayanyi, rashin aikin matasa da sauransu, inda yace dole jami’ar ta kawo dauki.

Shugaban jami’ar farfesa Aliyu Shugaba yace sunje masa murna ne gidan gwamnatin don rantsar dshi da akayia matsayin gwamnan jihar da kuma murnar sallah a matsayin su na mambobin jami’ar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *