Najeriya: Gwamnatin Jihar Borno Zata Gina Gadoji A Birnin Maiduguri

zuulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum zai fara ayyukan gina gadoji da dama a birnin Maiduguri don rage matsalar cinkoson jama’a a tituna.

Zulum ya ziyarci daya daga cikin guraren da za’a gina gadar inda yace za’a fara aikin cikin kan kanin lokaci inda za’a fara daga kasauwar waya wato Kasuwan Jogol zuwa asibitin birni, sai kuma wadda zata dauka daga sha tale-talen post office zuwa sha tale-talen Elkanemi wato kasuwa ta Monday Market.

Gwamnan bai fadi taka maimai yaushe za’a fara aikin ba amma ya bayyana cewa bazai dauki lokaci ba.

Haka nan bai bayyana lokacin da aikin zai dauka ba ko abinda za’a kashe ba.

Related stories

Leave a Reply