
By: Habiba Ahmed, Maiduguri
Gwamnatin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta samar da sababbin injinan janareta guda 2 masu karfin 750KVA da 1100KVA a kogin Alau domin ganin an kawo karshen matsalar ruwa a jihar.
Yayin da yake duba yadda ake hada injinan kwamishinan ruwa na jihar Zanna Abubakar Jabu ya godewa gwamna Kashim Shettima da yayi kokarin samar da wadan nan injinan guda 2 wadanda aka bukata don samarwa mutane saukin matsalar ruwa da ake fama da ita.
Haka nan ya godewa mutanen ma’aikatarsa a kokarin da sukeyi na ganin an gudanar da ayyuka yadda suka dace.
Ana dai fama da rashin ruwa a jihar inda a wasu guraren cikin birnin Maiduguri ake siyan ruwa har Naira 60.
Haka zalika an samu rashin wuta a kwanakin nan sakamakon harin da yan ta’adda suka kai kan grurin da ke samar da wutar dake kusa da kauyen Molai a jihar inji kwamishinan.
Dandal Kura sun gano yayin da suke zantawa da jama’a sun gano cewa irin haka ta taba faruwa ne fiye da shekara 15 da suka gabata.
