Najeriya: Gwamnatin Jihar Borno Ta Nada Sarkin Kano A Matsayin Shugaban Jami’ar Jihar

gwamnatin jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya ta nada sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban jami’ar jihar ta Borno.

mataimakin shugaban jami’ar farfesa Umar Kyari Sandade da rakiyar sakataren din-din-din na ma’aikatar ilimi ta jihar Borno da sauran shugabannin jami’ar ne suka kai masa takardar nadin ranar Asabar 22 ga watan Yuni na shekarar 2019 a fadarsa dake kano.

Sarkin Malam Muhammadu Sanusi dai shugaba ne a wata jami’ar dake jihar Edo a Benin, haka nan shugaba ne a jami’ar Skyline dake Kano, san nan kuma shugaba ne a jami’ar Ekiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *