Najeriya: Gwamnatin Jihar Adamawa Zata Samarwa Ma’aikata Gidaje 2000

adamawa-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamantin jihar Adamawa da hadin gwiwar Federal Government Housing Financing Agency da Family Homes Fund zasu samar da gidaje masu rukuni 2000 ga ma’aikatan jihar.

Aikin zai lakume kimanin Naira biliyan takwas kuma zai samar da ayyuka ga matasa kimanin 200 da kuma koyon ayyukan gini.

Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri yace ma’aikata 2000 zasu samu gidajen a fadin jihar inda ya kirayi Family Homes fund dasu bada lokacin da aikin zai kare.

Ya kara da cewa an dade a jihar ba a samar da gidaje ba fiye da shekara biyar, amma gwamnatinsa zata yi kokarin ganin ta kyautatawa jama’ar jihar, inda yace za’a samar da gidaje 1400 a birnin jihar, sai 300 a Mubi sai ragowar a sauran kananan hukumomin jihar.

Manajan Daraktan Family Homes Fund Mr Femi Adewoleyace aikin zai dauki kimanin wata 12.
BBW RGK/SFI/BBW

Related stories

Leave a Reply