Najeriya: Gwamnatin Jihar Adamawa Zata Mikawa Majalisar Jihar Kudiri Kan Masu Garkuwa Da Mutane

fintirii
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar adamawa dake Arewa maso gabashin Najeriya ta bayyana cewa zatamika kudirinta ga majalisar jihar kan a yanke sabuwar doka mai zafi da zata dinga hukunta masu garkuwa, yan fashi da kuma wadanda suke hada baki dasu.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da yayi a gidan Radiyo da Talabijin na jihar Adamawa inda yace za’a mika dokar da zarar an gama dubata.

Ya bayyana cewa kowa yasan babu wata al’umma da zata cigaba matukar akwai matsalar tsaro yankin, san nan ana dakile ta’addanci ne in dai gwamnati ta tashi tsaye.

Ya kara da cewa gwamnatin sa zata cigaba da bada taimako ga yan kungiyar sa kai da maharba wadanda jami’an tsaro zasu tantance don taimakawa sha’anin tsaro a yankin.

Gwamna Fintiri ya gargadi ma’aikatan dake rikon sakainar kasha ga ayyukansu inda yace ba kamar da bane dole su tashi tsaye.

Related stories

Leave a Reply