Najeriya: Gwamnati Bata Da Niyyar Cire Tallafin Mai – Zainab Ahmed

finance
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin kasar najeriya ta jaddada cewa bata da niyyar cire tallafin mai ko nan gaba. Ministan kudi Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan yayin wani taro da suka gudanar da masu zuba jari da mutanen bankin duniya a garin Washington DC dake kasar Amurka.

Ahmed ta bayyana cewa bankin duniya ne ya bawa gwamnati shawarar cire tallafin na mai don a samu ayi amfani da wasu ma’adanai a kasar, wanda haka ne ya yasa mutane suka tsorata.

Duk da shawara ce mai kyau amma gwamnatin Najeriya bata da niyyar cire tallafin man a yanzu saboda bamu shirya hakan ba.

Ta kara da cewa suna nan suna aiki da wasu kungiyoyi don a samo mafuta idan ana so mu cire tallafin.

Related stories

Leave a Reply