
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gayyaci wani Almajiri dan shekara 13-mai suna Usman zuwa ofishinsa.
Gwamnan ya gayyaci yaron bayan yaga labarin yaron a shafin Twitter bayan da wani ya wallafa a shafinsa, wanda hakan yaja hankalinsa.
Wanda ya wallafa din ya bayyana cewa Usman dan asalin jihar Borno ne, inda yace ya koyi aikin gyaran takalmin ne a wajen yayanshi inda yake samun kimanin Naira 500 a rana.
Usman yasha fadawa jama’a cewa yanaso ya dinga zuwa makaranta amma babu wanda zai dauki nauyinsa kuma abinda yake samu a rana bazai ishe shi yayi karatu ba.
El-Rufai ya bukaci a kawo masa yaron inda ya bayyana cewa a shirye yake ya taimawa yaron kan iliminsa.
