Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Nada Mai Bada Shawara Ta Fannin Tsaro Da wasu Mataimaka Na Musamman 10

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Colonel A.A. Chiroma a matsayin babban mai bada shawara ta fannin tsaro.

Babban mai bawa gwamnan shawara kan hulda da jama’a da tsare-tsare, Malam Isa Gusau ne ya bayyana hakan a rahoton da ya fitar a Maiduguri.

Haka nan gwamnan ya nada wasu mataimaka na musamman guda 10 wanda 2 daga ciki zasu yi aiki karkashin mataimakin gwamna.

Mutanen da aka nada sun hada da, Alh. Mustapha Ali mataimaki na musamman kan sha’anin tsaro, Ali Abba Jato mai kula da ayyukan ofishin Abuja, Mr. Christopher Godwin Akaba mataimaki na musamman kan samar da ayyuka da taimakawa matasa, sai Sale Habib mataimaki na musamman kan tsare tsare da harkar tarurrruka.

Ragowar sune Bukar Mustapha mataimaki na musamman kan daukar bayanai, Shuaibu Baba Adamu mataimaki na musamman kan yada labarai a ofishin mataimakin gwamna, Alfred Yahaya Bwala mataimaki na musamman kan mahimman ayyuka a ofishin mataimakin gwamna, Alhaji Mustapha Bulu kan kula da kudaden jama’a, Yusuf Usman Shettima mataimaki na musamman mai kula da ayyuka da tantancesu sai Abdullahi Yusuf kan daukan rahoton ayyuka.

Gusau ya kara da cewa Gwamna Zulum sai fitar da ranar rantsuwar masu bada shawara na musammnan nan ba da dadewa ba inda ragowar kawai zasu kama ayyukansu.

Related stories

Leave a Reply