Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Karyata Wasu Ayyukan Kungiyoyin NRC Da MCI A Jihar Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum dake arewa maso gabashin Najeriya ya karyata ayyukan da kungiyoyin sa kai na Norwegian Refugee Council da Mercy Corps International suka ce sun gudanar a jihar Borno na samar da ruwa da gidaje.

Inda suka ce sun gudanar da ayyukan na taimako wasu gurare a Jere, Gwozada kuma birnin Maiduguri.

An gano wannan ne bayan da shugaban kungiyar kasashen turai ya kaiwa Mr. Laban Onismas ya kaiwa gwamnan ziyara a fadar gwamnatin jihar dake birnin Maiduguri.
Umara yace bincike ya nuna cewa NRC sunyi 150, Mercy Corps kuma ta samar da rijiyoyi 350 ba gaskiya bane kuma binciken ya nuna gida daya kawai Mercy Corps tayi a Gwoza.

Haka nan ya bayyana cewa dole kowace kungiya a jihar Borno ta bawa gwamnati damar jan ragamar ayyukanta kuma ta dinga duba yadda suke bada taimakon ga mutane a jihar.

Ya kara da cewa duk wadda bata da niyyar bawa gwamnati hadin kai to ta shirya barin jihar.

Umara ya kara da cewa baza su karbi kudin shiga daga kungiyar hadin kan kasashen turai ba har sai gwamnati ba har sai sun bawa gwamnati damar jan ragamar ayyukansu na cigaba da kuma shirin su bayan an gama rikicin a yankin.

Ya bayyana musu cewa idan sun yarda da abubuwan da ya gindaya sai su cigaba da aiki idan kuma basu yadda ba zai rubuta wa kungiyar, idan basu yard aba a shirye suke su canza su.

Ya kara da cewa da cewa bankin duniya da bankin Afirika na bawa mutane taimako da hannu ya kamata kungiyoyin su dinga yi da gwamnati.

San nan ya yabawa kungiyar UNICEF kan taimakawa gwamnati da yan gudun hijira kimanin mutuum miliyan 2.7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *