
Rahoton da aka samu cewa yan kungiyar Boko Haram sun kawo hari yankin molai da jidari polo, ya jawo rudani a yankin wanda hakan yasa wadansu suka gudu suka bar gidajensu.
Bayan jin wan nan labari mara dadi gwamnan jihar Babagana Umara Zulum da rakiyar jami’an tsaro sun ziyarci yankin don ganewa idonsu inda suka tabbatar ba gaskiya a cikin labarin, kuma mutanen yankin na gudanar da al’amuransu yadda ya kamata.
Gwamnan ya bayyana cewa zai kafa kungiyar bada agajin gaggawa da zasu dinga kula da kawo agaji cikin sauri da kuma bada taimakon gaggawa yayin da aka kawo hari.
San nan ya kirayi mazauna birnin Maiduguri musamman wadanda ke wajen birnin dasu kiyayi yada jita-jita.
