Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Kaddamar Da Gidaje 400

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya kaddamar da gidaje 400 a karamar hukumar Mafa dake jihar. Haka nan Gwamnan yasa harsashin ginin wasu gidajen 400 a yankin Ajiri.

San nan ya kaddamar da rabon kayan aikin noma ga ‘yan gudun hijirar dake garin. Haka nan Zulum ya duba yadda aiki yake gudana na gyaran Dikwa Holiday Resort inda ya bada umarnin a maida shi gurin koyan sana’oi.

Haka nan ya ziyarci wasu kananan hukumomi don ganin yadda aikin noma yake tafiya a yankunan musammman rabon kayan noma. San nan ya duba aikin hanya da akeyi wanda ya hada da kana nan hukumomin Mafa, Dikwa da Ngala inda yace idan aka gama aikin zai habbaka harkar cinikayya a yankin da kasashen dake makotaka kamar Kamaru, Nijar Chadi.

Haka nan ya yabawa hukumar gyaran hanya ta jihar da ma’aikatar ayyuka kan kokarin da sukeyi, inda yayi alkawarin za’a gama aikin duka gyaran hanyoyin nan da shekaru biyu zuwa uku.

Haka nan ya roki gwamnatin tarayya data gyara babbar hanya ta Maiduguri zuwa Bama zuwa Banki da Maiduguri zuwa Gamboru-Ngala. .

Related stories

Leave a Reply