Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Gudanar da Bikin Sallah A sansanin Gudun Hijira

zuulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya farfesa Babagana Umara Zulum ya gudanar da bikin sallah a sansanin yan gudun hijira a sansanoni daban daban inda ya raba musu kudi, kayan sawa, abinci.

Zulum ya samu tarba daga shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jiha Yabawa Kolo da kuma dubban yan gudun hijira a sansanin dake teacher’s village a birnin Maiduguri.

Gwamnan ya bayyanawa yan gudun hijirar cewa sun san halin da suke ciki kuma suna kan aikin yadda za’a maida su garuruwansu cikin kankanin lokaci.

Mutane 350 da suka zo kwan nan nan daga Doron sun samu kyautar 5000 ko wanne, da shinkafa, gishiri, zani, kuma an tabbatar za’a gia musu gidaje da zasu zauna.

Haka nan ya gargadi manajan sansanin kan raba kayan yadda ya dace.

Related stories

Leave a Reply