Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Gana Da ‘Yan gudun Hijira Dake Diffa A Nijar

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno ta samar da buhunhunan hatsi 10,000 don saukakawa mutane da suke gudun hijira ayankin Diffa dake jamhuriyar Nijar.

Gwamnan ya bayyan hakan yayin da yake ganawa da ‘yan gudun hijirar jihar Borno da sukaje daga abadam, mobbar da guzamala zuwa jamhuriyar Nijar.

Farfesa Zulum ya tabbatar da cewa suna nan suna kokarin yadda zasu dawo da yan gudun hijirar gida bada dadewa ba.

Gwamnan ya samu tarba daga gwamnan Diffa Alh mohamed modu, wanda ya godewa gwamnatin Najeriya wajen kula da ‘yan Najeriya dake gudun hijira a Diffa.

Ya kara da cewa gwamnatin kasashen 2 zasu duba hanyoyi masu sauki wajen samun hanya mai kyau daga Damasak zuwa Diffa ta hanyar cinikayya da zirga zirga.

Haka nan farfesa Babagana umara Zulum ya bayyana cewa zai bada Naira miliyan 10 ga ‘yan gudun hijirar dake Diffa inda yace Miliyan 5 daga gwamnatin jihar ne, miliyan 3 daga sanata Habu kyari sai 2 miliyan daga Hon. Bukar Gana mamba mai wakiltar yankin a majalisar kasar.

Related stories

Leave a Reply