Najeriya: Gwamnatin Jihar Adamawa Zata Karbi ‘Yan Najeriya 4,000 Daga Kasar Kamaru

Gwamnan jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta karbi ‘yan Najeriya 4,000 dake gudun hijira a kasar Kamaru.

Da yawansu sun gudu zuwa kasar kamaru ne sakamakon rikicin Boko Haram wanda ke addabar Arewa maso gabas kimanin shekaru 10.

Yayin da yake ganawa da kungiyar shirin dawo da ‘yan gudun hijirar Fintiri ya bayyana cewa gwamnatin sa zata kafa kwamiti da zai taimaka wajen dawo da ‘yan gudun hijirar.

Kwamishinan majalisar dinkin duniya na UNHCR, Najeriya da Kasar Kamaru sun yi yarjejeniya kan dawo da ‘yan gudun hijirar wanda ke kasar Kamaru tun shekarar 2017.

Mutane jihar Adamawa sun ragu sosai sakamakon ‘yan gudun hijirar da fiye da mutane 50,000 suke a kasar Kamaru a sansanin dake Minawo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *