Najeriya: Gwamantinmu Ta Bada Mahimmanci Kan Samar Da Ruwa – Zulum

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyan cewa gwamnatinsa ta bada mahimmanci a samar da ruwan sha don tabbatar da samun ruwa isasshe mai mai tsafta da mutane da dabbobi zasu sha.

Farfesa Zulum ya bayyana hakan yayin kaddamar da gurin samar da ruwa na Alamdairi wanda ICRC da ma’aikatar ruwa ta jihar Borno suka samar.

Gwamnan ya kara da cewa ruwan na Alamdairi na da matukar mahimmanci ga gwamnatin jihar Borno shi yasa gwamnatin ta bada mahimmanci ga karasa aikin.

Haka nan gwamnan ya kara da cewa ICRC ta shiga tarihin jihar Borno a kokarin da suke na samar da ayyukan cigaba a Arewa maso gabashin Najeriya musamman jihar Borno.

San nan ya bayyana ruwan Alamdairi a matsayin mai mahimmanci inda ake sa ran zai samar da ruwa lita 90,000 a kullum inda lita 60 zai iya amfanar mutane fiye da 150,000 a kullum.

Haka nan ya kirayi ma’aikatar ruwan da tayi duk abinda ya kamata wajen ganin an kula da kayan aikin yadda ya dace.

A yayin da yake jawabi shugaban tawagar ICRC a Najeriya, Mr. Eloi Fillion ya bayyana cewa ruwan Alamdairi zai amfani fiye da mutane 80,000 da ‘yan gudun hijirar dake birnin Maiduguri.

Related stories

Leave a Reply