
By: Babagana Bukar Wakil Ngala
Gwamnan jihar Borno dake Arewa maso gabashin najeriya farfesa Babagana umara zulum Ya kai ziyarar aiki karamar hukumar Bama inda ya kwana a can. Bama dai na daya daga cikin garuruwan da suka fuskanci matsalar Boko Haram a yankin.
Gwamnan ya ziyarci makarantar umar lbn lbrahim wadda Boko Haram suka lalata inda ya bukaci a sake gina makarantar a fara karatu a wan nan shekarar.
Zulum ya zagaya dakunan dalibai da suka lalace, gidaje 20, makarantar technical college da kuma GGSC duk a garin Bama inda duk Boko Haram suka bata.
Ya tabbatar da cewa zai bawa yan asalin jihar duk su gyara duk makarantu da guraren da suka lalace.
Haka nan ya ziyarci babban asibiti da aka gyara wanda da yan gudun hijira ke zaune a ciki inda tsohon kwamishinan lafiya Dr Salish kwaya bura ya zagaya dashi, Gwamnan ya yaba da aikin asibitin inda ya bukaci da a samo kayan aiki na zamani a dinga karbar haihuwa kyauta kuma a fara aiki dashi.
