Najeriya: Guraren Shan Magani Kashi 30 Kadai Suke Aiki A Jihar Borno – WHO

Mayakan Boko Haram sun lalata gurare shan magani da illata ma’aikatan lafiya da dama a Arewa maso gabashin Najeriya wannda ya haifar da rashin samun alluran rigakafi na cututtuka da suke hallaka yara da sauki kamar su kwalara.

Kimanin guraren shan magani kashi 45 suka lalata a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda wasu baza su sake amfani ba.

Kungiyar lafiya ta duniya wato WHO ce ta bayyana hakan a hutun mako a rahoton da ta fitar na shekarar 2018 a Maiduguri.

Kashi 30 ne kadai suke aiki a jihar Borno, Adamawa 45 sai 69 a jihar Yobe. Sun kara da cewa an lalata maganin cizon sauro fiye da na mutum 3,000 a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno.

Rahoton na WHO ya tabbatar cewa cikin guraren shan magani 755, an lalata 292 (kimanin kashi 39) sai 205 da aka lalata rabinsu (kamar kashi 27).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *