Najeriya: Gobara Ta Lashe Dakuna 140 A Sansanin Yan Gudun Hijira A Borno – NEMA

By: Babagana Bukar Wakil

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta bayyana cewa anyi gobara a matsugunan yan gudun hijira guda biyu a karamar Monguno dake jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya inda mutane 140 suka rasa dakunan su.

Mai yada labarai na hukumar NEMA, Malam Abdulkadir Ibrahim, ne ya fitar da rahoton ranar Lahari a birnin Maiduguri.

Ibrahim ya bayyana cewa gobarar ta faru a sansanin Flatari da Nguro dake Monguno ranar Asabar.

Ya kara da cewa 28 a Flatari inda ya shafi magidanta 20 sai 120 na magidanta 77 a Nguro, inda mutane 371 suka rasa matsugunansu a sansanin guda biyu.

Ibrahim yace hukumar na nan na binciken yadda gobarar ta faru da musabbabinta. Haka nan hukumar ta hada kai da hukumar SEMA don taimakwa wadanda abun ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *