Najeriya: Fiye Da Wadanda Akayiwa Fyade 10,000 Ne Aka Kwantar Musu Da Hankali – SARC

SARC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kimanin wadanda a akayiwa fyade 10,000 ne aka kwantar musu da hankali a rahoton da aka fitar na cew kimanin kashi 60 ne akayiwa fyaden a  Nigeria inda yawanci yara ne daga watanni zuwa shekaru 14. Inda kashi 15-20 na wadanda suka rayu maza ne.

An bayyana hakan ne a taron da aka gudanar kashi na 5 a taron cibiyar da ake tura wadanda abin ya shafa a najeriya, inda aka gudanar da taron a Abuja wanda Daraktan kasa na Pathfinder International, Dr. Farouk Jega ya jagoranta.

Taron na kwana 3 ya kawo masu ruwa da tsaki inda suka tattaua akan matsalolin dake addabar, nasara da neman ilimi da kafuwar SARCs a Nigeria.

Jega Ms. Favour Adam’s, ce ta wakilci jega inda tace SARC na matukar taimakon asibitoci a kasar inda suke bada taimako ta hanyar bada magani, sauya tunani wadanda abun ya shafa da bin kadin ciwukan wadanda abun ya shafa.

Ya kara da cewa ayyukan SARC nada amfani sosai inda ake amfani da binciken da sukayi a kotu da kuma yadda abun ya faru.

Ya kuma bayyana cewa cibiyar na cike wasu gurabu inda take da yankuna a gurare 15 a jihohin Adamawa, Akwa-Ibom, Anambra, Borno, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Lagos, Niger and Yobe states.

Related stories

Leave a Reply