Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: EFCC Sun Kama Mutane 8 Da Suke Sayarda Gubataccen Takin Zamani A Gombe Da Bauchi

efcc-operatives
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ofishin shiyya na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama mutane 8 saboda suna gurbata takin zamani da siyar dashi a cikin garin Gombe da kauyen Lariski dake karamar hukumar Kirfi a jihar Bauchi.

Wadanda ake zargin sun hada da Usman Shawari, Adamu Abdulhamid, Dahiru Salisu, Dahiru Muhammad, Abdullahi Maidawa, Suleman Ahmed, Muhammed Aliyu da Ibrahim Musa.

Acewar hukumar, wadan nan mutanen sun kware wajen siyan taki daga kamfanoni masu inganci sai su juye su zuba Yashi su sashi a ainihin buhun taki mai tambarin kamfani ba tare da neman izinin kamfanin ba san nan kuma su siyar a kudin da kamfanin yake sayarwa.

Hukumar na gargadin musamman manoma dasuyi hattara kuma sukai rahoton irin wadan nan miyagun mutanen domin a hukunta su.

Related stories

Leave a Reply